Kenya na barazana ga FIFA

Gwamnatin kasar Kenya ta ce a shirya take ta fuskanci dakatarwar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, idan ta karbe ikon gudanarda harkar kwallon kafa a kasar.

An dade ana takaddama tsakanin FIFA da kuma hukumomi a Kenyan, game da wanda ke da ikon tafiyarda harkar kwallon kafa a kasar.

Ministan Wasanni a kasar Otuoma Nyongesa, ya ce bai amince da yadda ake gudanarda harkar wasanni a kasar ba.

"Mun shaidawa FIFA cewa ta daidaita al'umuran kwallon kafa a kasar, kuma idan sun gagara yin hakan, mu zamu dauki alhakin yin hakan da kanmu."

Idan har gwamnatin kasar Kenya ta karbe ikon gudanarda kwallon kafa a kasar, akwai yiwuwar hukumar ta FIFA za ta dakatar da Kenya daga harkokin kwallon kafa a duniya.

Dokokin FIFA sun haramtawa gwamnatoci tsoma bakinsu a harkar kwallon kafa.