Siasia ne sabon kociyan Najeriya

Siasia
Image caption Akwai kalubale babba a gaban sabon kocin na Super Eagles

Najeriya ta nada Samson Siasia a mtsayin sabon kocin kungiyar Super Eagles, amma hakan zai dogare ne kan kwantiragin da za a sanyawa hannu a 'yan kwanaki masu zuwa.

Siasia mai shekaru 43, kwamitin kwararru na hukumar kwallon kafa ta kasar NFF ne ya zabe shi, bayan ya tantance tsakanin shi da Stephen Keshi.

Siasia wanda ya taba zama kociyan kungiyar kwallon kasar 'yan kasa da shekaru 20 da 23, ya maye gurbin Austin Eguavoen wanda ke rike da kungiyar na wucin gadi.

Ana saran zai fara aiki a ranar 1 ga watan Disamba, inda zai maida hankali kan kokarin kai kasar gasar cin kofin kasashen Afrika.

Cancanta

A ranar Alhamis, hukumar NFF ta bada sanarwa inda ta bayyana dalilan zabar Siasia kan Keshi.

Sanarwar ta ce: "bayan dogon tunani da tattaunawa, hukumar NFF ta amince da shawarar da kwamitin kwararru ya gabatar mata na nada Samson Siasia a matsayin kociyan Super Eagles."

"Sai dai hakan zai dogare ne kan kwantiragin da za a sanyawa hannu a 'yan kwanaki masu zuwa."

Nadin na Siasia ya kawo karshen dadewar da aka yi ana jiran tsohon dan wasan ya zamo kociyan kungiyar ta Super Eagles.

Siasia ya dade yana tattaunawa da NFF kan wannan aiki, kafin hukumar ta yanke shawarar tallata aikin, abinda yasa Keshi ya zamo kishiyarsa a neman.

Bayanda ya lashe gasar matasan kasashen Afrika, Siasia - wanda tsohon dan wasan Lokeren da Nantes ne, ya kai matasan kasar zuwa wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 a shekara ta 2005.

Ya kuma kai tawagar kasar zuwa wasan karshe na gasar motsa jiki ta Olympic a shekara ta 2008.

Rahotanni sun nuna cewa za a dinga biyansa kudaden da suka ta samma naira miliyan biyar a kowanne wata.

Kalubale

Babban kalubalen da ke gaban sabon kocin dai shi ne ya dawo da martabar kasar a fagen kwallon kafa na Afrika dama duniya baki daya.

Tare da tabbatar da cewa Super Eagles ta ci gaba da mamaye harkar kwallon kafa a nahiyar Afrika, kamar yadda ta saba a baya.

Da yake magana bayan tabbatar da nadin nasa, Siasia ya shaidawa mujallar Kick-off cewa zai maida hankali ne wajen sauya yadda 'yan wasan na Super Eagles ke taka leda.

Sannan ya yi alkawarin maido da martabar kasar kamar yadda aka santa a fagen kwallon kafa a duniya.

Zargin cinhanci da rashawa

Hukumar kwallon Najeriya ta samu kanta cikin badakala da kuma zargin cinhanci da rashawa bayanda kasar ta taka mummunar rawa a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Afrika ta Kudu.

Abinda yasa hukumar yaki da cinhanci da rashawa ta EFCC gurfanar da tsaffin shugabannin hukumar a gaban kuliya.

Har ila yau rikicin shugabanci ya sa kasar fuskantar fushin Hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA, wanda sai a makon da ya gabata ne aka sasanta. Najeriya ta kori Ahmadu Shu'aibu a watan Fabrerun da ya gabata, sannan ta dauki Lars Lagerback dan kasar Sweden, watanni hudu kafin fara gasar cin kofin duniya.