Fernando Torres ya yiwa Chelsea tsiya

Image caption Fernando Torres bayan ya zura kwallo a ragar Cheslea

Liverpool ta doke Chelsea a filin anfield da ci biyu da nema.

Fernado Torres ne ya zura kwallayen biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Chelsea tayi ta kai hare-hare bayan an dawo hutun amma bata samu rama kwallo ko guda ba.

Duk da cewa dai an doke Chelsea a wasan, har yanzu dai itace ke ci gaba da jagoranci a kan tebur a gasar ta Premier da maki ashirin da biyar, a yayinda Manchester United ke biye da ita da maki 23.

Nasarar da Liverpool din ta samu ya kara mata matsayin a kan tebur, inda ta taso daga matsayi na goma sha biyu, zuwa matsayi na tara.