Manchester United ta sha da kyar a hannu Wolves

Image caption Kwallo na biyu da Park Ji-sung ya zura

Park Ji-Sung ya zura kwallaye biyu, inda ya taimakawa Manchester United a nasarar datayi a kan Wolves.

Park dai ya zura kwallon da ta ba Manchester United nasara ne a karin lokacin bayan kungiyoyin biyu sun buga minti casa'in da wasan cif-cif.

Park ne ya fara zura kwallon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan kuma bayan dan dawo Sylvan Ebanks-Blake ya fanshewa Wolves.

Wolves dai ta barar da kwallaye da dama kafin Manchester ta lashe wasan a karin lokaci.

Sai da kuma dan wasan Manchester Owen Hargreaves wanda ya kwashe shekaru biyu yana jinya ya samu buga wasan, amma dai bai kaiga buga minti shiga a wasan ba, kafin ya sake samun wani raunin.