FIFA ta karawa mai tsaron gidan Togo kyautar kudi

Image caption Kodjovi Obilale

Mai tsaron gidan tawagar kwallon kafar Togo Kodjovi Obilale zai samu kyautar dala dubu dari daga hukumar FIFA domin jinyar harbin da aka yi masa a lokacin gasar cin kofin Afrika a watan Janairun da ya gabata.

A watan Satumbar da ya gabata ne dai Shugaban FIFA Sepp Blatter ya yiwa Obilale alkawarin cewa FIFA za ta bashi dala dubu ashirin da biyar daga asusunta domin ya yi jinya.

Daga baya ne dai kuma Hukumar ta sauya ra'ayin karawa dan wasan kudi.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25 yana jinyar harbin bindiga ne da aka yi masa a bayansa da kuma cikinsa, a harin da aka kaiwa tawagar Togo a Angola a lokacin da suke kan hanyar su na halartar gasar cin kofin Afrika da aka shirya a kasar.

Ma haran dai sun kashe mutane biyu a harin da aka kaiwa Tawagar ta Togo.