Santa Cruz na son barin Manchester City

Image caption Roque Santa Cruz

Roque Santa Cruz ya shaida wa BBC cewa ya kammala shawarar barin kungiyar Manchester City a watan Janairu, saboda rashin takawa kungiyar leda.

A watan Okutoban da ya gabata ne dai kocin City Roberto Mancini ya ce zai yi wuya dan wasan ya samu shiga gurbin 'yan wasa goma sha daya da za su rika samun damar taka leda a ko wane lokaci..

"Bana ganin zan iya samu damar bugawa a matakin farko a kungiyar, kuma wannan al'amari na ci mun tuwo a kwarya." In ji Santa Cruz.

"Tun da kocin kungiyar ba shi da kwarin gwiwa a kaina, ba zan iya matsa mai ya sani a wasa ba."

Santa Cruz dai ya zura kwallaye 23 a wasanni 57 da ya buga a lokacin da yake takawa kungiyar Blackburn leda kafin ya koma City a shekarar 2009, inda kungiyar ta saye shi a kan fam miliyan 17.5.