Bolton ta samu faduwa da fam miliyan 35

Kungiyar Bolton dake taka leda a gasar Premier ta Ingila na ci gaba samun faduwa a hannun jarin kungiyar.

Kungiyar dai ta samu faduwa wanda ya ninka faduwan datayi a kakar wasan bara, saboda sauya mai horadda da kungiyar da kuma siyan 'yan wasa.

Alkaluman asusun kungiyar a karshen watan yuni sun nuna cewa kungiyar ta samu faduwan daga fam miliyan13.2 zuwa fam miliyan 35.4.

Wannan dai ya hada da kudin sallaman tsohon kocin kungiyar Gary Megson wanda ya kai fami miliyan 4.2 da kuma dauko wanda ya maye gurbin shi Owen Coyle daga kungiyar Burnley.

Har wa yau dai kungiyar ta sayi sabbin 'yan wasa kuma ta karawa wasu albashi.