Zulqarnain Haider ya nemi mafakar siyasa a Ingila

Image caption Zulqarnain Haider

Dan wasan Kruket na Pakistan Zulqarnain Haider ya nemi mafakar siyasa a Ingila, bayan ya bada sanarwar yin murabus daga wasan na kruket.

Dan wasan Kruket din dai ya yi layar zana ne, inda aka nemi shi aka rasa a Otal din da kasar ta sauka a Dubai a ranar Litinin, bayan wasan da kasar ta buga da Afrika ta kudu.

Dan wasan yac e dai wasu mutane na neman ya siyarda wasan da kasar ta buga da Afrika ta kudu, inda suke barazana ga rayuwarsa.

Haider dai ya gudo daga Pakistan inda ya koma Ingila, inda ake ganin zai nemi mafakar siyasa.

Ya ce: "Yafi dacewa in daina buga wasan kruket, domin kare rayuwar iyali na, ana yawan barazana ga rayuwata saboda wasan."