Redknapp ya mayarwa magoya bayan Spurs martani

Image caption Kocin Tottenham Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya mayarwa magoya bayan kungiyar martani bayan sun yiwa 'yan wasa ihu, bayan da aka kammala wasan da kungiyar ta buga da Sunderland inda aka tashi daya da daya.

A yanzu haka dai Spurs ta dawo na shida a kan tebur a gasar ta Premier, bayan ta gagara samun nasara a wasanni hudu da ta buga a gasar a jere.

Redknapp yace: "Ban san abun da suke wa ihu ba."

"Kwallon da kungiyar take bugawa a yanzu, ba'a taba buga irinta a tarihin kungiyar ba, bai kamata ace wasu na nuna bacin rai game da rawar da muka taka ba."

Redknapp harwa yau ya soki alkalin wasa Howard Webb, inda ya zarge shi da hana kungiyar fenareti da kuma kin sallamar dan wasan Sunderland Lee Cattermole.