Beckenbauer ya ce zai bar kujerarsa a kwamitin zartarwar FIFA

Image caption Franz Beckenbauer

Shahararen tsohon dan wasa da kuma Kocin Jamus Franz Beckenbauer ya ce zai bar kujerarshi a kwamitin zartarwar FIFA, domin samun lokacin kula da iyalinsa.

Beckenbauer ya ce ba zai tsaya zabe ba a badi, domin baya so yana yawan tafiye tafiye.

Ya ce; " Inda da kyakyawan alaka da sauran membobin kwamitin na FIFA da kuma UEFA, kuma ina zumunci da Sepp Blatter da kuma Michel Platini."

Wa'adin kujeran Beckenbauer na tsawon shekaru hudu zai kare ne a a farkon shekara ta 2011.