Ghana za ta fuskanci fushin FIFA

Image caption Abedi Pele

Gwamnatin Ghana ta tsayar da Abedi Pele domin tsayawa takarar kujerar kwamitin zartarwa na hukumar kula da kwallon Afrika, wato CAF.

Ghana dai ta sanya Shugaban hukumar kwallon kafar kasar da ya janye takarar da yake yi, inda kuma ta maye gurbinsa da Abedi Pele.

A watanni ukun da suka wuce ne dai hukumar kwallon Ghana ta zabi shugabanta Kwesi Nyantakyi domin tsayawa zabe a badi abin da kuma Hukamar CAF ta amince da shi.

Harwa yau dai Ma'ikatar kula da wasannin kasar ta nemi hukumar kwallon kafar Ghana da ta sauya sunan shugaban dana Abedi Pele.

FIFA dai ta haramtawa gwamnotoci tsoma bakinsu, a harkar kwallon kafa, kuma masana na ganin katsa landa din da gwamnatin Ghana tayi na iya fuskantar fushin FIFA.