Najeriya ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Afrika ta mata

Image caption Tawagar Falcons

Tawagar Falcons ta Najeriya ta tsallake zuwa wasan karshe a gasar cin kofin Afrika ta mata da kasar Afrika ta kudu ke karban bakonci.

Najeriyar dai ta lallasa kasar Kamaru ne da ci biyar da guda a wasan kusa dana karshe da kungiyoyin biyu suka buga a yau.

Najeriya dai ta lashe gasar sau biyar a baya. kuma zata buga wasan karshe ne da wadda tayi nasara tsakanin tawagar kasar Afrika ta kudu da kuma mai rike da kambun gasar wato Equatorial Guinea, wanda za su fara a dan an anjiman nan.