Aston Villa ta buga kunnen doki da Manchester United

Image caption Aston Villa 2 Man United 2

Manchester United ta samu ta farke kwallaye biyu da Villa ta zura mata, inda aka tashi biyu da biyu.

Ashley Young ne ya fara zura kwallon farko a ragar United a bugun daga kai sai mai tsaron gida, kafin Marc Abrighton ya zura.

Sai Federico Macheda wanda ya fanshewa United kwallo guda kafin Nemanja Vidic ya farke ta biyu.

Machester United ta buga kunnen doki a wasanni biyu data buga a jere kenan bayan ta tashi babu ci tsakaninta da City, a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a tsakiyan mako.