Tawagar Falcons ta lashe gasar cin kofin Afrika ta mata

Image caption Tawagar Falcons

Tawagar Falcons ta Nigeria ta lashe gasar cin kofin Afrika ta mata da kasar Afrika ta kudu ta karbi bakonci.

Najeriyar ta doke Equatorial Guinea ne da ci hudu da biyu a wasan karshe da kungiyoyin biyu suka buga.

Perpetua Nkwocha da Ugochi Oparanozie sun zura kwallo guda kowannanensu a wasan, a yayinda, Equatorial Guinea ta zura kwallaye biyu a ragar ta sannan ta zura biyu a ragar Najeriya.

Equatorial Guinea dai ce ta fidda Najeriya a wasan kusa dana karshe a gasar da kasar ta karbi bakoci shekaru biyu da suka wuce.

Najeriyar dai ta lashe duk wasanni da ta buga a gasar ta bana