Roberto Mancini ya kare dabarunsa

Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya kare dabarun dayake amfani dasu wajen tafiyar da kungiyar a yayinda kungiyar ta buga canjaras sau biyu a jere.

Manchester City ta buga canjaras da Birmingham a wasan da ta buga a ranar asabar, bayan ta tashi babu ci a wasan tsakiyan mako da ta buga da Manchester United.

Magoya bayan kungiyar dai sunta ihu bayan an sauya Carlos Teves da Gareth Barry a lokacin da aka kusan kammala wasan.

Mancini ya ce: "Takaici ya dame ni nima. Ina son in samu nasara. Ba'a son raina muke buga canjaras ba."

Ya ce, ya sauya Tevez ne saboda dan wasan na fama da rauni.

Mancini ya kara da cewa: " Na ga idan na sauya shi da wani dan wasan zamu fi samu damar zura kwallo."

"Magoya bayan kungiyoyi duk haka suke ko, a Ingila da Italy, duk so suke ai ta sa 'yan wasan gaba, wanda kuma ba koda yaushe dabarar ke tasiri ba."