Sunderland ta lallasa Chelsea

Image caption Chelsea 0 Sunderland 3

Cheslea ta sha kashi ne a filin Stamford Bridge da ci uku da nema.

Onuoha ne ya fara zura kwallo farko a ragar Chelsea kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan kuma bayan an dawo ne da minti bakwai Asamoh Gyan ya zura ta biyu.

Sai kuma Welbeck da ya rufe wasan da ta uku ana sauran minti uku a tashi.

Duk da da cewa dai Chelsea ta sha kashi a wasan haryanzu ita ke ci gaba da jagoranci a gasar ta Premier da maki 28, a yayinda Arsenal ke biyeda ita da maki 26.