Ingila ta nisanta kanta da zargin jami'an FIFA

Image caption Shugaban kwamitin neman daukar bakonci gasar kofin duniya ta 2018 a Injila, Mista Geoff Thompson

Kwamitin da Ingila ta kafa na neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2018, ya rubutawa FIFA wasika inda ta nisanta kanta da rohatannin cin hanci a kan wasu jami'an FIFA da wata Jaridar kasar ta buga.

Kwamitin dai ya nemi Hukumar FIFA da kada tayi la'akari da rahoton na jaridar Sunday Times wajen zaben kasar da ta dace, a maimakon haka kamata ya yi a yi amfani da cancantar ta.

Wasikar da ta samu sa hannu Shugaban kwamitin Thompson da kuma David Dein, wani kokari ne da kasar ke yi na ceto yunkurinta na karban bakuncin gasar cin kofin duniyar ta 2018.

Ana dai hasashen cewa Ingila na iya fuskantar fushin jami'an hukumar FIFA, wajen zaben kasar da ta cancanci daukar nauyin gasar, saboda rahotannin cin hanci da Jaridar Sunday Times ta buga kan wasu Jami'an FIFA biyu.

FIFA za ta kada kuri'ar neman kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da kuma 2022 a ranar 2 ga watan Disamba.