Capello ya kare matakin amfani da Gerrard na tsawon lokaci

Image caption Kocin Ingila, Fabio Capello

Kocin Ingila Fabio Capello ya kare matakinsa na barin Steven Gerrard a filin wasa na tsawon minti 85 a wasan sada zumuncin da Faransa ta doke Ingila da ci biyu da daya.

Gerrard dai ya samu rauni a wasan daya buga, abin da kuma yasa daya daga cikin masu horon 'yan wasan Liverpool Darren Burgess ya soki Capello saboda barin Gerrard da yayi na tsawon lokaci a wasan.

Amma Capello ya ce: "Na shaidawa Liverpool cewar zai buga wasa na tsawon sa'a guda ne."

"Gareth Barry da Rio Ferdinand duk suna fama da rauni muna bukatar manyan 'yan wasa a fili. Ban ji dadin abun da ya faru da Gerrard ba."

Capello ya kara da cewa: "Basu da 'yancin gaya min tsawon wa'adin da zanyi amfani da dan wasan."