Bani da niyar ajiye aiki. - In ji Alex ferguson

Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce yana da burin ci gaba da horon kungiyar Manchester United har na tsawon wani lokaci.

Ferguson dai zai cika shekaru 69 da haihuwa a watan Disamba kuma ya ce bashi da niyar ajiye aiki a Manchester United, kungiyar da ya fara horo tun a shekarar 1986.

"Ya ce ajiye aiki na matasa ne," In ji Ferguson. "Na tsufa da batun ajiye aiki, saboda idan nayi hakan babu abun da zanyi."

"Idan har ina da koshin lafiya, zan ci gaba da aiki."