Har yanzu AC Milan ce kan gaba a Serie A

Zalatan Ibrahimovic
Image caption Zalatan Ibrahimovic na ci gaba da haskakawa a Milan

Kungiyar AC Milan na ci gaba da haskakawa a gasar Serie A, bayanda ta lashe Fiorentina da ci daya mai ban haushi.

Zalatan Ibrahinmovic ne ya zira kwallon a minti na 45 da fara wasan.

Wannan nasara ta ba su damar kasancewa a saman teburin Serie A da maki 29.

AS Roma na ci gaba da farfadowa bayanda ta doke Udinese da ci biyu da nema a filin wasa na Stadio Olympico.