Eto'o na fuskantar dakatarwa a Italiya

Image caption Samuel Eto'o

Kungiyar Inter Milan za ta san matsayinta a ranar talata, ko za'a a dakatarda dan wasanta Samuel Eto'o bayan ya yiwa wani dan wasa karo.

Eto'o ya yiwa dan wasan Cheivo Bostjan Cesar karo ne a kirji a wasan da kungiyar ta buga da Inter Milan.

"Abin da Eto'o ya yi na iya sanya a hukunta dan wasan, ina dai fatan babu ambin da zai faru". In ji Shugaban Inter Massimo Moratti.

Hukumar kwallon kafan Italiya ta ce za ta kalli hoton bidiyon wasan domin tabbatarda abin da ya faru, sannan ta dau hukunci.

Idan dai an samu Eto'o da laifi, za'a iya dakatarda shi na tsawon wasanni biyu zuwa hudu a Italiya, kuma dakatarda dan wasan na iya kawo cikas ga kocin Kungiyar Rafeal Benitez, saboda yana fuskantar rashin 'yan wasan gaba saboda suna fama da rauni.