Hukuncin FIFA kan Adamu ya yi tsauri-Mong-joon

Chung Mong-joon
Image caption Duka Amos Adamu da Raynald Tamarii sun musanta zargin

Mataimakin shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Chung Mong-joon, ya ce hukuncin da hukumar ta yanke na dakatar da mambobin kwamitinta na zartarwa kan zargin keta doka ya yi tsauri.

A ranar Alhamis ne kwamitin da'a na hukumar kwallon kafa ta FIFA, ya dakatar da Amos Adamu na Najeriya daga harkokin kwallon kafa har tsawon shekaru uku, sannan ya ci tarar sa dala 10,000.

Kwamitin ya kuma dakatar da Reynald Temarii na kasar Tahiti, wanda shi ma mamba ne a kwamitin zartarwa na hukumar tsawon shekara guda, tare da tarar dala 5,000.

Kwamitinta na da'a na FIFA ya same su da laifin yunkurin sayar da kuri'unsu a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da 2022.

Chung ya ce yana da ja kan cewar abin da mutanen suka aikata bai kai girman da za a yanke musu wannan hukuncin ba.