Al Ahly ta nada sabon koci

Image caption Tsohon kocin Al Haly, Hossam Al Badry

Kungiyar Al Ahly ta kasar Masar ta bayyana sunan tsohon dan wasanta Abdel Aziz Abdel Shaf a matsayin sabon kocin kungiyar.

Sabon kocin zai maye gurbin Hossam Al Badry, wanda ya yi murabus a karshen mako bayan da Ismaili ta doke kungiyar.

Abdel Shafi zai yi aiki ne da Abdel Hafeez, wanda shi ma tsohon dan wasan kungiyar ne, wanda kuma zai zama daraktan kwallon kafa a kungiyar.