Mataimakin Kocin West Ham ya yi murabus

Image caption Zeljko Petrovic

West Ham ta bada sanarwar cewa mataimakin kocin kungiyar Zeljko Petrovic, ya bar kungiyar.

Petrovic, mai shekarun haihuwa 45, wanda kuma dan kasar Montenegro ne, ya bar kungiyar ne bayan ya yi aiki da ita na tsawon watanni hudu.

West Ham dai ce a kasan tebur a gasar Premier ta Ingila, inda ta lashe wasa daya tilo a kakar wasan bana a gasar ta Premier.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Karren Brady ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar kocin kungiyar Avram Grant zai ci gaba da aiki da ita a karshen kakar wasan bana.