Fabregas da Eboue sun samu rauni

Image caption Cesc Fabregas

Arsenal na fuskantar matsala bayanda Emmanuel Eboue da Cesc Fabregas suka samu rauni a wasan da kungiyar ta buga a gasar zakarun Turai.

Kungiyar Braga dai ta doke Arsenal da ci biyu da nema, abin da kuma yasa dole sai Arsenal din ta yi nasara a wasan karshe kafin ta samu wucewa zuwa zagaye na biyu.

Fabregas dai ya samu rauni ne a cinyarsa, sai kuma Eboue da ya turgude gwiwarsa.

"Fabregas ba zai taka leda ba na tsawon makwanni biyu, zuwa uku." In ji Arsene Wenger.

Wenger dai ya sanya Fabregas ne a wasan, duk da cewa dan wasan bai gama murmurewa ba.