An dakatar Suarez na tsawon wasanni 7

Image caption Luis Suarez

Hukumar kwallon kafar Holland ta dakatarda Kyaftin din Ajax Luis Suarez na tsawon wasanni bakwai bayan ya ciji dan wasan PSV Eindhoven Otman Bakkal a kafadarsa a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a karshen mako, inda suka tashi canjaras.

Tun farko dai, Kungiyar shi ta Ajax, ta ci tarrar dan wasan kuma ta dakatar da shi na tsawon wasanni biyu.

Suarez dai ba zai samu taka leda ba a Holland sai a watan Fabrairun Badi, amma dai zai iya taka leda a Turai.

Saurez ne dai ya tare kwallo da hannunsa kafin ya shiga raga a wasan kusa dana karshe da kasarshi ta Uruguay ta buga da Ghana a gasar cin kofin duniya da aka kamala a kasar Afrika ta kudu, Inda Uruguay din tayi nasara a bugun fenarity.