Arsene Wenger ya soki tsarin alkalan wasa a Turai

Image caption Kocin Arsenal Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya soki tsarin amfani da alkalan wasa biyar a gasar zakarun Turai, bayan an hana kungiyar shi fenareti a wasan da ta buga da Braga.

A lokacin da kungiyoyin ke tafiya babu ci, Arsenal ta nemi a ba ta fenareti bayan an tade Carlos Vela amma dai maimakon haka sai alkalin wasan ya nuna masa katin gargadi.

Wenger, ya ce hana kungiyar fenaretin ne ya haddasa kashin da ta sha inda Braga ta doke ta da ci biyu da nema.

"Akawai alkalin wasan da ke bayan raga, bansan dalilin da ya sa ya hana mu fenareti ba."