Ferguson ya jinjina wa Rooney

Wayne Rooney
Image caption Wannan ce kwallon shi ta farko tun bayanda ya dawo daga jinya

Kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson ya yaba wa kwarin guiwar da Wayne Rooney ya nuna wurin buga fanaretin da ya baiwa United damar doke Rangers da ci 1-0.

Sakamakon wasan dai ya nuna cewa United ta tsallake zuwa zagaye na biyu duk da cewa a kwai wasa daya da ya rage.

"A na bukatar kwarin guiwa sosai kafin mutum ya iya buga wannan fanaretin," in ji Ferguson.

"Wasan ya zo wa Rooney da tsauri domin ya zubar da damar-maki, amma mun yaba da kokarinsa". Kwallo dayan da a ka zira a wasan dai ta zo ne ta hanyar fanareti minti biyar kafin wasan ya kare, bayan da Steve Naismith na Rangers ya ture Fabio da Silva na United.

Abin da ya baiwa Rooney damar zira kwallon shi ta farko tun bayanda ya dawo daga jinyar raunin da ya yi fama da shi.