Federer ya kai wasan kusa dana karshe a gasar ATP

Image caption Roger Federer

Roger Federer ya lashe duk wasanni da ya buga a gasar ATP da ake yi a Landon, domin kai wa matakinn wasan kusa dana karshe.

Federer wanda shine na biyu a duniya ya doke Robin Soderling ne a wasan dab da kusa dana karshe.

Roger Federer ne a yanzu haka ke jagoranci a rukunin B, bayan nasarar da ya yi, kuma zai buga ne da wanda ya yi nasara tsakanin Andy Murray da kuma David Ferrer.