Tottenham za ta fadada filin wasan ta

Image caption Filin wasa na White Hart Lane

Magaji garin Landon Boris Johnson ya baiwa kungiyar Tottenham damar fadada filin wasanta ta White Hart Lane.

Magajin garin na Landon dai ya sauya matakin da karamar hukumar Haringley ta dauka na hana Kungiyar fadada filin wasanta zuwa mai wurin zama 56,000.

Kungiyar spurs dai za ta kashe wurin fam miliyan dari hudu da hamsin wajen fadada White Hart Lane.

Har wa yau dai Spurs ta nuna bukatar ta na neman komawa filin wasa na Olympic dake Landon a shekara ta 2012.