Rooney ya ce bashi da niyyar komawa Man City

Image caption Wayne Rooney

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya karyata rohotannin dake nuni da cewa yana da niyar komawa kungiyar Manchester City.

Rooney, mai shekarun haihuwa 25, ya yi yunkurin barin kungiyarshi ta United a makon daya gabata, saboda an kasa cimma matsaya game da sabon kwantaraginsa a kungiyar.

Daga baya dai, Rooney ya amince yarjejeniya da kungiyar United, inda ya sa hannu a kwantaragi na tsawon shekaru biyar.

Daga bisani dai Rooney ya baiwa magoya bayan kungiyar hakuri, saboda yadda yaki sabonta kwantaraginsa da farko.

"Idan har na bar Manchester United, to ba zan koma wata kungiya ba a Ingila. Jita jitan da ake yi cewa zan koma Manchester City bashi da tushe." In ji Rooney.