BBC ta zargi wasu Jami'an FIFA da karbar cin hanci

Image caption Ricardo Teixeira da Issa Hayatou da kuma Nicolas Leoz

Shirin BBC na Panaroma ya zargi jami'an FIFA uku da za su kada kuri'a a zaben kasar da ta cacanci ta karbi bakoncin gasar cin kofin duniya, da za'a shirya a shekarar 2018 da kuma 2022 da cin hanci.

An zargi Nicolas Leoz da Issa Hayatou da kuma Ricardo Teixeira da karban cin hanci daga wani kamfanin kasuwanci, a shekarun alif dari tara da casa'in.

Kudin da ake zargin jami'an sun karba a matsayin cin hanci zai kai kimanin dala miliyan dari.

Jami'an uku dai ba su amsa zargin da shirin ya yi musu ba. Harwa yau dai ita ma hukumar Fifa, taki tayi hira da shirin da shirin game da jami'an na ta.