Hayatou ya musanta zargin cin hanci

Image caption Issa Hayatou

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika, Issa Hayatou ya musanta zargin cin hanci da wani shirin talabijin na BBC ya yi inda aka zarge shi da wasu jami'an FIFA biyu da karbar cin hanci daga wani kamfani a shekarun alif dari tara da casa'in.

Mista Hayatou, wanda har wa yau yana rike da mukamin mataimakin Shugaban hukumar FIFA ya ce, yana duba yiwuwar kai BBC kara kotu, saboda bata masa sunnan da tayi.

Shirin na Panorama ya ce Jami'in ya karbi kimanin Fam dubu goma sha biyu da dari tara a shekarar 1995 daga wani kamfanin kasuwancin wasannin da ake kira ISL, a matsayin goron neman kwangiloli.

Mista Hayatou ya ce kudin da ya karba na aiwatarda da wata yarjejeniya ne na talla da kamfanin ya kulla da CAF.

"Kudin bana kashin kaina bane, amma na CAF." In ji Hayatou.

"Ina tattaunawa da Lauyoyi na kuma ina ganin zan shigar da kara."