Ingila 2018: Beckham na da kwarin gwiwa

Image caption David Beckham

Dan wasan Manchester United David Beckham ya ce yana da kwarin gwiwa FIFA za ta baiwa Ingila damar daukar bakoncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.

FIFA dai za ta kada kuri'ar kasar da ta dace ta dauki nauyin bakoncin gasar a ranar alhamis a birnin Zurich.

Akwai fargabar da ake yi na cewa rahotanni da wasu kafafen yadda labarai ke watsawa a Ingila kan batun zargin cin hancin akan wasu jami'an FIFA na iya sauya yadda jami'an za su kada kuri'ar kasar da ta dace.

Beckham ya ce: "Na yarda da jami'an gabaki daya, kuma ina da kwarin gwiwa cewa za su yi abin da ya dace."

Tsohon kyaftin din Ingila Beckham ya na birnin Zurich ne tare da Prince William da kuma Fira Ministan Burtaniya, David Cameron domin neman kamun kafa.