UEFA ta dakatar da Jose Mourinho

Image caption Jose Mourinho

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai ta dakatar da kocin Real Madrid Jose Mourinho na tsawon wasanni biyu a gasar zakarun Turai.

Hukumar ta kuma ci tarar kocin dala dubu hamsin da biyu, saboda ta same shi da laifin rashin bin ka'aidar wasa a gasar zakarun Turai a wasan da kungiyar ta lallasa Ajax da ci biyar da nema.

An samu Mourinho ne da laifin sanyan 'yan wasan sa biyu, a basu katin sallama da gangan domin su samu buga wasan kifa daya kwalla.

UEFA har wa yau ta ci tarar 'yan wasan biyu wato Xabi Alonso da Sergio Ramos,dala dubu 26.