Portsmouth za ta kai Inter Kotu kan Muntari

Image caption Sulley Muntari

Kungiyar Portsmouth da ke Ingila ta ce za ta shigar da kara kotu a kan Inter Milan saboda ta keta yarjejeniyar Siyan Sulley Muntari.

Portsmouth ta zargi Inter Milan da kin biyan sauran kudaden da aka cimma yarjejeniya a kan Muntari.

Shugaban kungiyar ta Portsmouth Andrew Andronikou ya ce wa'adin da kungiyar ta debar wa Inter Milan ya wuce da dade wa kuma har yanzu Inter Milan ba ta cika alkwari ba.

Portsmouth ta ce za ta shigar da kara a Italiya, domin neman a biya ta bashin da take bin Inter Milan wanda ya kai fam dubu dari tara.