Ancelotti ya rude bayan Everton ta rikesu a kunen doki

Chelsea
Image caption 'Yan Chelsea sun koma addu'a don neman nasara

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti na cigaba da fuskantar matsin lamba baya kungiyar ta buga kunen doki tsakaninta da Everton.

A halin yanzu dai Chelsea ta samu maki biyar ne kacal daga wasannin gasar premier shida data buga kuma ta kasa samun nasara a wasanni hudu a jere.

Ancelotti yace" mun tsorata ne bayan da 'yan kwallon Everton suka fara kai hare hare.

Nan gaba dai Chelsea zata hadu ne da Tottenham da Manchester United da kuma Arsenal.

Chelsea wacce ta lashe gasar premier a kakar data wuce ta samu nasara a wasanninta biyar na farko a kakar bana inda ta zira kwallaye 21 amma a kwannan ta shiga rudu inda take ta uku akan tebur sannan da kyar take kwantan kanta a gasar.