Magajin Garin London ya kalubalanci Fifa

Johnson
Image caption Magajin Garin London Boris Johnson ya daga tuta a London

Magajin garin birnin London Boris Johnson ya janye kyautar makwancin da akayiwa jami'an Fifa alkwari na zama a otal a kyauta lokacin gasar Olympics ta 2012.

Magajin garin ya yiwa shugaban Fifa Sepp Blatter da 'yan tawagarshi alkawarin basu kyautar makwanci lokacin gasar Olympics, amma bayan da Ingila ta samu kuri'a biyu kacal daga cikin 22 don neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018, sai Magajin garin ya canza sharawa.

Rasha ce dai aka baiwa damar daukar bakuncin gasar.

Kawo yanzu dai magajin garin bai ce komai ba game da wannan hukuncin daya dauka.

Tun bayan da Ingila ta sha kaye dai, Mista Johnson wande yaje Zurich da kanshi don kamun kafa wajen jami'an Fifa ya nuna bacin rai akan yadda Ingila ta kasa samun damar.