Owen ya koma horo bayan jinyar watanni biyu

Man u
Image caption 'Yan wasa Red Devils suna horo a Old trafford

Michael Owen ya shiga cikin horo da sauran 'yan kwallon Manchester United a shirye shiyensu na tunkarar Valencia a ranar Talata a gasar zakarun Turai.

Ciwon kafada yasa dan kwallon bai kara taka leda ba tun ranar biyu ga watan Oktoba, amma ana saran zai zauna a benci a karawarsu da Valencia.

Shima Paul Scholes ya shiga horon amma dai dan kwallon baya Jonny Evans bai shiga ba saboda rauni.

Golan United Edwin van der saar yace" duk da cewar mun tsallake zuwa zagaye na gaba amma muna son samun nasara saboda kasancewa na farko a rukunin".