Martin Jol ya yi murabus a matsayin kocin Ajax

Jol
Image caption Akwai alamun Martin Jol zai koma Newcastle

Martin Jol ya yi murabus a matsayin kocin Ajax ta Holland bayanda kungiyar ta kasa taka rawar gani a kakar wasa ta bana.

Tsohon kocin Tottenham ya bar Ajax Amsterdam ne bayan 'yan wasanshi sun tashi kunen doki tsakaninsu da NEC Nijmegen.

Ajax za ta kara da AC Milan a ranar Laraba a gasar zakarun Turai amma dai kungiyar ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Jol na daga cikin wadanda ake hasashen za a baiwa mukamin kocin Newcastle bayan korar Chris Hughton a ranar Litinin.

Jol me shekaru 54 ya horadda Tottenham a 2004 zuwa 2007 kafin a maye gurbinshi da dan Spain Juande Ramos.

Jol ya koma Ajax a kakar wasan data wuce inda ta kasance ta biyu akan tebur, sannan kungiyar ta lashe gasar kofin Holland ta kuma tsallake zuwa gasar zakarun Turai.