2018:Blatter ya ce Ingila ta ki daukar kaddara

Blatter
Image caption A lokacin da Blatter ya bayyan Rasha a matsayin kasar da zata dauki bakuncin gasar

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Sepp Blatter ya ce Ingila taki daukar kaddara bayan Rasha ta samu damar ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018.

Blatter kuma yayi facali da zargin cin hanci akan Fifa bayan da Ingilan ta samu kuri'u biyu kacal cikin ashirin da biyu na jami'an Fifa.

Blatter yace yaji mamakin Ingila nata korafi bayan tasha kaye. Ingila wacce itace uwa ma bada mama a harkar kwallon kafa.

Blatter ya bayyanawa jaridar Swiss cewar " bai kamata bayan an kamalla komai kazo kace anyiwa Ingila alkawarin wasu kuri'u bayan ga sakamako ya fito".

Wasu daga cikin tawagar 'England 2018' sun ji mamaki saboda jami'an Fifa da dama sunyi alkawarin bada kuri'arsu amma basu cika ba.