Platini yace kada Faransa ta kara kiran Anelka da Evra

Platini da Beckham
Image caption Platini da David Bechkam na Ingila suna jituwa sosai

Shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa a Turai Uefa Michel Platini ya ce kamata yayi 'yan kwallon da suka jawowa Faransa abun kunya lokacin gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a daina kiransu har su bar kwallo.

Platini ya ce kwata kwata 'yan kwallon basu nuna dattaku ba kuma basu da amfani bayan sun kauracewa horo sakamakon korar Nicolas Anelka da kocin yayi.

Koch Raymond Domenech ya kori Anelka gida ne bayan Mexico ta casa Faransa daci biyu da nema, sannan daga bisani aka dakatar da dan kwallon na wasanni 18.

Hukumar kwallon Faransa har wa yau a wani matakin labadtar da sauran 'yan kwallon da suka yi bore shine ta dakatar da tsohon kaptin dinta Patrice Evra daga buga wasanni biyar, sai Franck Ribery aka dageshi wasanni uku a yayinda Jeremy Toulalan shi kuma wasa guda.

Platini na daga cikin tawagar Faransa data lashe gasar cin kofin kasashen Turai a shekarar 1984 amma a lokacin da aka bashi dama a matsayin koci sai ya kasa taka rawar gani.