Akwai shakku akan Scholes zai buga wasan United da Arsenal

Scholes
Image caption Scholes ne jagoran tsakiyar United

Akwai tababa Paul Scholes ba zai buga karawar da Manchester United zata yi da Arsenal ba a ranar Litinin mai zuwa, in ji Sir Alex Ferguson.

Dan shekaru talatin da shida din dai rabonshi daya taka leda tun a watan daya wuce.

Scholes ya kasance kashin bayan United a kakar wasa ta bana inda ya taimaka mata ta kasance ta biyu akan tebur.

A halin yanzu dai dan kwallon bayan United Rio Ferdinand ya turgude kuma shima akwai ayar tambaya akan makomar lafiyarshi.

Rashin Scholes dai ya nuna cewar Anderson na damar cigaba da fara wasa a United.