Ni ne nafi dacewa da Chelsea, in ji Ancelotti

Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti yana fuskantar matsin lambar

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya hakikance shine mutumin da yafi dacewa ya jagoranci kungiyar duk da tangal tangal din da suke yi a kakar wasa ta bana.

Chelsea dai ta samu nasara ne a wasa guda cikin karawa shida a gasar premier sannan kuma abubuwa suka kara cakudewa bayan da Marseille ta dokesu daci daya me ban haushi a gasar zakarun Turai.

A halin yanzu kuma zasu hadu da Tottenham da Manchester United da Arsenal a wasanni uku a jere, amma dai Ancelotti ya ce zasu shawo kan matsalar.

Yace"zamu koma yadda muke a baya, kuma zan maida hankali akan aiki na".

Chelsea saboda tangal tangal ta koma ta uku akan tebur daga ta farko.