Fifa ta yi barazanar dakatar da Ghana a harkar kwallon kafa

Blatter
Image caption Fifa ta haramtawa gwamnati tsoma baki a kwallon kafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya fifa ta gargadi gwamnatin Ghana akan cewar ta daina tsoma baki a harkar kwallon kasar koma a dakatar da Ghana daga shiga gasar kwallo a duniya.

Sanarwar fifa din na zuwa ne bayan da jamian yaki da rashawa a Ghana suka kai samame a shalkwatar hukumar kwallon kasar wato gfa inda suka tafi da wasu kayayyakin aiki.

Fifa ta ce an mika batun ga kwamitin gaggawa mai iko saka takunkumi kuma daga nan zuwa ranar Lahadi idan abubuwa basu canza ba za a dauki hukunci.

Sanarwar ta ce Fifa ta amince ayi bincike akan kudaden da gwamnati ta baiwa Gfa amma banda wadanda Fifa ko Caf suka bayar