An shawarci Fifa ta canza lokacin gasar kwallon duniya a Qatar 2022

Qatar
Image caption Lokacin da Sepp Blatter ya bayyana Qatar a matsayin wacce za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya na 2022

Tsohon sakatare janar na hukumar kwallon nahiyar Asiya, Peter Velappan ya bukaci Fifa ta canza lokacin da za a gudanar da gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar saboda tsananin zafi.

A cewarshi saboda zafin na kaiwa ma'aunin celsios arba'in,hakan ka iya jawo babbar matsala ga 'yan wasa.

Velappan yace kamata yayi amadai gasar watan Junairun a memakon watan Yuni ko Yuli.

Ya kara da cewar shirin sanyaya filayen wasa da wajajen horon 'yan kwallo ba zai magance matsalar zafin ba.

Velappan ya gargadin cewar wasu kasashen Turai zasu kauracewa gasar saboda zafin.

Ra'ayin Velappan yayi daidai dana wani babban jami'in Fifa Franz Beckenbauer wanda a farkon wannan watan shima ya bada shawarar canza lokacin gasar cin kofin duniya sau daya tal a 2022 don kada a wahal da 'yan kwallo.