Drogba na fatan Chelsea za ta dawo kan ganiyar ta

Image caption Didier Drogba

Dan wasan Chelsea, Didier Drogba, ya ce yana fatan Chelsea za ta dawo kan ganiyar ta a wasan da za ta buga da Tottenham ranar Lahadi.

Kungiyar ta samu maki hudu ne kacal cikin wasanni shida da ta buga a gasar Premier, a yayinda kuma ta koma a matsayi na uku a kan tebur a gasar.

Kungiyar ta Chelsea ta kuma sha kashi a gasar zakarun Turai a wasan da ta buga da Marseille a ranar Laraba da ci daya mai ban haushi.

Drogba ya ce: "Jama'a da dama na ganin za a doke mu a wasan da za mu buga a ranar Lahadi, amma ina ganin zamu fidda kan mu kunya."