Blackburn Rovers ta kori kocin 'yan kwallonta Sam Allardyce.

Allardyce
Image caption Allardyce ne koci na biyu cikin wannan watan da aka kora a premiership

Kungiyar Blackburn Rovers ta Ingila ta kori kocin 'yan kwallonta Sam Allardyce.

An sallame Allardyce da mataimakinshi Neil McDonald ba tare da jin kiri ba.

Blackburn ta sha kashi a wasanninta uku cikin biyar data buga hadda na ranar Lahadi inda Bolton ta bata kashi.

Sanarwa daga Rovers ta ce "mun yanke shawarar ce a matsayin wani tsari na ciyar da kungiyar gaba".

A halin yanzu dai Blackburn Rovers ce ta goma sha uku akan teburin gasar Premier League.

A nada Steve Kean a matsayin kocin na riko.