Kulob kulob na Ghana zasu koma taka leda

Ghana
Image caption 'Yan kwallon Black Stars sun taka rawar gani a gasar cin kofin duniya

Kungiyoyin kwallon kafa na Ghana sun amince su koma buga kwallo bayan dakatar da gasar da suka yi a makon daya gabata.

Kungiyoyi sun kauracewa buga kwallonne don nuna rashin jin dadinsu akan yadda hukumar yaki da cin hanci ta Ghana takai samame a shakwatar hukumar GFA.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa tayi gargadin daukar hukuncin idan har ba a koma gasar kwallo a kasar ba.

A yanzu kungiyoyi sun amince su koma taka leda kuma zasu buga gasar cin kofin FA a ranakun Talata da Laraba.

A wani labarin kuma, an bude shalkwatar hukumar Gfa a ranar Litinin a karon farko bayan samamen da aka kai mata.