Dan kwallo ya mutu a gasar premier ta Najeriya

NPL
Image caption Gasar premier ta Najeriya na juyayi

Wani abun tausayi ya faru a gasar kwallon Najeriya a karshen mako bayanda dan kwallon baya na Ocean Boys' Emmanuel Ogoli ya mutu bayan ya suma a cikin fili.

Take aka dauki Ogoli zuwa asibiti amma tun kafin su isa asibitin sai rai yayi halinshi.

Ogoli ya fadi kasa ne minti talatin da tara da fara wasa tsakaninsu da Niger Tornadoes a filin Samson Siasia dake Yenagoa, inda a karshe aka doke Tornadoes daci biyu da nema.

A baya dai Ogoli yaji rauni a wata Nuwamba lokacin karawarsu da Plateau United kuma komowarshi fili keda wuya a karshe mako sai ya gamu da ajalinshi.

Kawo yanzu ba a san abinda ya kashe Ogoli ba, amma dai ana samun karuwar 'yan kwallo masu fama da ciwon zuciya.